ITEM 1

Kewaye a shafin J24

Abinda ke ciki


SHAFIN LABARAI CIKIN HARSHEN HAUSA DAGA JIGAWA24


Daya daga cikin Sanatocin jihar Kaduna ya caccaki El-Rufa’i, ya kira shi takadari
Ana rububin sayen rigar Super Eagles a Ingila
Mutane da dama ne ke son su mallaki sabuwar rigar da 'yan wasan Super Eagles za su saka a gasar cin kofin duniya a Rasha. Gwamman mutane ne suka yi layi a harabar ofishin Nike a titin Oxford, da ke Landan, kafin a bude ofishin da safe domin su samu sayen rigar 'yan kwallon na Najeriya. Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta bayyana cewar har an biya kudin rigar Super Eagles, sama da miliyan uku gabannin fitowarta. Magoya bayan tawagar kwallon kafar Najeriyar, sun shaida wa BBC cewar sun tafi shagon na Landan ne bayan sun ji cewar an gama sayar da kayan a shafin intanet. Suna da damar sayen riga biyu ne kawai daga shagon na Landan, kuma da yawa daga cikinsu suna neman ko rigar wasan gida ko kuma ta wasan waje wadanda suka kai kudi naira dubu talatin da daya (£64). Steven Chester, dan Ingila amma dan asalin Najeriya, ya ce shi yana son ya samu rigar ne kafin wasan sada zumunta da za a yi tsakanin Super Eagles na Najeriya da Ingila. Ya ce rigar ta tuna masa da rigar shekarun 1990 wadda aka yi amfani da ita a gasar Firimiya "kuma wannan lokacin ne ake da kayan kwallon mafi kyau," in ji shi. "Yana da kyau sosai a ga Najeriya a fagen wasan kallon duniya." Christina Tubes, wadda ta fara bin layi tun karfe shida na safe, ta ce ita ba ta samu ta saye rigar a intanet ba ne shi ya sa ta fito domin sayen rigar a yanzu. Ta yi ikirarin cewa ita magoyi bayan tawagar Najeriya ce ta gaske, amma ta ce ba ta ji dadin rashin kayan kwallon na mata da kanana yara ba. "Wannan ya bata mini rai, domin ni magoyi bayan Najeriya ce ta gaske kuma shi ya sa nake a nan," in ji ta. Damola Timeyin, mai shekara 33, wanda ke aiki a wani kamfanin talla ya shaida wa BBC cewar a matsayinsa na dan Najeriya, zai ji dadin samun rigar. "A matsayi na mai rike da fasfo din Najeriya, ina ganin nauyin da ya rataya a kai na ne in samu rigar domin gasar cin kofin duniya." "A gaskiya tawagar Najeriya ita ce za ta kasance tawagar da ta fi ko wacce kyau a gasar cin kofin duniya, ina fatan tawagarmu za ta wuce matakin rukuni-rukuni domin mu saka wannan rigar zuwa mataki na sili daya kwale," in ji shi. Za a fara gasar cin kofin duniya ne a Rasha ranar 14 ga watan Yuni.

CALL or SMS


80s toys - Atari. I still have