DUBUNNAN MUTANE SUN YI
GANGAMI DON MURNAR
DAWOWAR SHUGABA BUHARI
A JIHAR JIGAWA

Dubunnan al'umar Jihar
Jigawa ne suka fito tituna
domin nuna farin cikin su ga
dawowar Shugaban Ƙasa
Alhaji Muhammadu Buhari
daga jinyar da ya tafi na fiye
da wata a birnin London.



Titunan garin na Dutse ya ga
dubunnan al'uma da suka fito
don nuna farin ciki da godiyar
su ga Allah, wanda hakan ya
ƙara tabbatar da cewa
masoyan da Shugaban Ƙasan
ke da shi ƙaruwa suke.
"Dawowar Shugaba Buhari
abin farin ciki ne da ya
cancanci ayi murna, kamar
yadda kuka sani Shugaban
Ƙasan da Mataimakin sa suna
ɗaukan duk matakai da suka
dace domin farfaɗo da
tattalin arzikin mu da ya
taɓarɓare. Buƙatar mu shine
Shugaban Ƙasan da
Mataimakin sa suci gaba da
yaƙi da cin hanci da rashawa
da ƙwato mana haƙƙoƙin mu
da gurɓatattun Shugabannin
baya suka wawashe" a cewar
ɗaya daga cikin waɗanda
suka haɗa taron kuma
Shugaban Matasan Jam'iyyar
APC na Jiha Haruna Danzomo.
Taron wanda aka fara daga
Ofishin Jam'iyya na Jiha ya
samu halartar masoya
Shugaban Ƙasan daga
Ƙananan Hukumomin Jihar
27 waɗanda suke ta kaɗe
kaɗe da raye raye da waƙoƙin
"Oyoyo Baba", "Ga Buhari ya
dawo" inda suka zagaye
lunguna da saƙunan garin na
Dutse.
Haka ma wani daga cikin
waɗanda suka shirya taron
Bashir Gumel yace "dole mu
cigaba da yiwa Shugaban
Ƙasa addu'ar samun ƙarin
lafiya domin ya samu ya
cigaba da yaƙi da masu tada
ƙayar baya a ƙasar nan. Mun
yi matuƙar farin ciki kuma
zamu cigaba da yi masa
addu'a".
Sauran Mahalarta Taron da
mazauna garin na Dutse da
aka tattauna da su sun
bayyana farin cikin su da
dawowar Shugaban Ƙasa da
samun lafiyar sa.
A ƙarshen zagaye da
gangamin an kada bajimin sa
da aka masa zanen Oyoyo
Baba domin liyafa.
Taron ya samu halartar
Shugabannin Jam'iyya,
Mashawarta da Mataimaka na
Musamman ga Maigirma
Gwamna, wasu masu riƙe da
muƙamai da dubunnan
jama'a.



This post has no comments - be the first one!