
Wani tsoho ya yanke jiki ya fadi da jin labrin Buhari ya dawo daga jinyar da ta kai shi birnin Landan
-Wannan ya zo ne a lokacin da dubban mutane ke murna da bikin dawowar shugaba Buhari wasu har da yanka kaji da raguna da kuma sauran dabbobi
Ibrahim a lokacin da ya suma za a kai shi asibiti
Karin maganar Hausawa da ke cewa, idan wasu sun ki ka da kwana, wasu da shekara suke neman ka ta tabbata a mararrabar Jos a ranar Juma'a.
A ranar 10 ga watan Maris shekarar 2017, ranar da shugaba Buhari ya dawo kasar nan, wani dan Shi'a ya yanke jiki ya fadi a sume bayan jin labarin dawowarsa yana tsaka da sauraron rediyo.
A cewar Hausa Press 24 mai yada labarai a dandalin sada zumunta na intanet, mutumin mai suna Ibrahim dan shekara 58, na sana'ar sayar da dankali a garin Mararrabar Jos.
A lokacin da ya ke tsaka da sauraron rediyonsa a tashar BBC, ya kuma ji labarin dawowar shugaban, sai ya buga rediyon da kasa, kafin ya yanke jiki ya fadi a sume.
Rahoton ya cigaba da cewa, an garzaya da tsohon asibiti, ko da ya ke ba a bayar da halin da ya ke ciki ba daga nan.
Tun bayan da 'yan Shi'a suka yi arangama da sojoji a garin Zaria ne, wanda hakan ta kai ga tsare shugabansu Ibrahim El Zakzaky, 'yan mazhabin suke ganin bakin shugaba Buhari.
Hakan a cewar rahotanni, ta sa 'yan Shi'ar tashi tsaye da addu'oin ganin cewa shugaban bai dawo da ransa kasar ba.
Dubban mutane ne suka kwarara kan titi musamman a arewacin Najeriya don nuna murnarsu ta dawowar shugaban a safiyar ranar Juma'a.
Ga wani hoton bidiyo na bikin dawowar Buhari



This post has no comments - be the first one!