
A yau Alhamis, 9 ga watan Maris, Sultan na Sokoto, Alhaji Saad Abubakar III, yayi kira da gwamnatin tarayya ta cire takunkumin hana shigo da shinkafa da motoci.
Ka cire takunkunmin hana shigo da shinkafa da motoci – Sarkin Musulmi ga Osinbajo
Sultan yayi wannan bayani ne lokacin da mukaddashin shugaban kasan ya kai masa ziyara fadarsa da ke jihar Sakkwato.
Sultan yace:“ Zamu cigaba da Magana da yawun talakawa a hanyar, muna kira ga gwamnatin tarayya tayi dubi cikin wasu sabbin dokoki da ta sanya wanda ke tsananta rayuwan yan Najeriya.
” Yan Najeriya na cikin mawuyacin hali kuma wadannan dokoki kada su kara tsananta azaban yan Najeriya."
KU KARANTA: Atiku ya gana da wani sarkin gargajiya
” Wannan zai kare kiyayya tsakanin shugabanni da wadana ake shugabanta.”
Sultan ya bada misali da takunkumin da aka sanya na haramta shigo da shinkafa da motoci ta iyakokin Najeriya inda yace a cire wannan takunkumi.”
Sarkin musulmin ya bada tabbacin goyon bayansa, addu’a da shawara ga gwamnati inda yace:
“Muna tabbatarwa wannan gwamnati cewa muna goyon bayanta, kuma zamu cigaba sa neman cigaban yan Najeriya."
Sarkin musulmin ya taya mukaddashin shugaban kasan murnan cika shekaru 60, yayi masa maraba zuwa shekarun tsufa.
Mukaddashin shugaban kasan ya nuna muhimmancin jiha Sakkwato a cikin al’amuran Najeriya kuma ya bada tabbacin cewa gwamnati zata cigaba da samar da cigaba da aikin noma domin fadada tattalin arzikin kasa.



This post has no comments - be the first one!