Farfesa Uwaleke ya bada shawaran a rage shigo da kaya daga kasashen waje

Wani masanin tattalin arziki, Farfesa Ubhe Uwaleke, ya baiwa yan Najeriya shawaran cewa su rage shigo da kayayyaki daga kasashen wajen domin karfafa darajar Naira a kasuwan duniya.
Darajar Naira: Masanin tattalin arzikin ya bada shawaran a rage shigo da kaya daga kasashen waje
Uwaleke wanda, shine shugaban makarantan ilimin banki da kudi na jami’ar jihar Nasarawa ya bayyana wannan ne ga NAN a wata hira da aka gudanar a yau Alhamis.
“ Ina sa ran ganin ragin shigo da kayayyaki Najeriya da kuma habakan tattalin arziki bisa ga Karin asusun raran kudi da kuma Karin darajar Naira a kasuwan bayan fagge,”.
KU KARANTA: An daure kato mai fyade a jihar Kano
Uwaleke yace sabon dokar canjin da babban bankin Najeriya CBN tayi, anyi shi ne domin tabbatar da cewa mutane zasu iya samun canji a sauki a kasuwan bayan fagge.
Yace wannan mataki zai rage bambancin kudin canji a bankuna da kuma bayan fagge.
“Samu a cigaba da wannan ya danganta da ka’idojin kasuwan main a duniya da kuma kudin danyen man fetur."
“Kana kuma ya danganta da cigaban zaman lafiya a yankin Neja Delta wanda ya taimaka kwarai,”
Dirkatan sadarwa da CBN, Mr Isaac Okorafor, yayi bayani a ranan Talata cewa bankin zata kara fito da $100,000 000 zuwa kasuwan canji.



This post has no comments - be the first one!